Tuesday 20 May 2014

E-COPY OF TSUNTSU OUR HAUSA NEWSPAPER ( MAY PUBLICATION)









DANDALIN DARIYA

Daga Abubakar Yusuf Mada

              Ba Mu Daga Cikin Matattu


A wani kauye ne wasu yara guda biyu suka saci mangoro a cikin buhu. Sai suka tsaya shawarar
inda za su tafi su raba ba tare da kowa ya gansu ba. Sai daya ya bayar da shawarar a tafi
makabarta.
Bayan sun isa makabarta dauke da mangoron nan, a kofar shiga sai mangoro biyu ya fado daga
cikin buhun, amma saboda suna sauri kada agansu sai suka bar su nan suka wuce cikin makabartar da sauran mangoron.
Su na shiga sai suka zube mangoron a kasa suka fara rabawa, babban ne ya ke rabo, sai ya dauki
mangoro daya ya aza a gabanshi ya ce, Ni dayasai kuma ya dauki daya ya aza a gaban karamin ya ce, Kai daya.Haka suka ci gaba da rabonsu. Can sai ga wani mashayi ya fito daga cikin daji wajen shaye shayensa, yana zuwa dai dai kofar makabarta sai
ya ji wata yar karamar murya kamar ta yara ana cewa, Kai daya, ni daya, kuma anci gaba da
maimaitawa. Sai kawai ya garzaya da sauri sai gidan limamin kauyen.

Yana zuwa ya same shi kofar gida yana shirin yin alwalar magariba. Ya ce, Allah gafarta malam,
yau wani bakon alamari ke faruwa a makabartar can. Na ji ana rabon matattu. Sai liman ya ce muje in gani.Su na zuwa, sai suka labe a bakin kofar makabartar, sai suka ji ana cewa, Kai daya, ni daya, kai daya, ni daya…” Can sai suka ji ance,To kai ga yawan naka nan, ni ga yawan nawa nan. Can kuma sai suka ji an kara cewa, To wadan can biyun na bakin kofar shigowa fa? sai suka ji daya ya ce, To mu je a dauko su mana.

Haba! Ai liman da mashayin nan na jin haka, sai suka ari takalmin kare, su na fadin ai mu ba mu
mutu ba, ba mu daga cikin matattu, tsammani suke yi da su ake, ba su san cewa yaran nan mangoron su biyu da suka fadi bakin kofa suke nufi ba.



                        Fatalwa

Wani saurayi ne da gidansu ke kusa da makabarta, kullum idan ya hawo mota ko babur baya biya, ana zuwa daidai makabartar nan sai ya ce a sauke shi, ana sauke shi sai ya nuna ai shima mataccene, fatalwa ya yi ya fito yawon shakatawa, kawai sai ya shige makabartar.Ana cikin haka ne wata rana ya hawo babur din wani dan achaba me shegen naci, bayan sun zo daidai makabartar sai saurayin nan yace, Tsaya na sauka anan yana sauka sai yai kokarin shiga
makabarta kamar yadda ya saba, amma sai Dan achaba ya rike shi ya ce ya ba shi kudinsa, to
anan ne saurayin nan ya ce da shi shi fa fatalwa ne ba me rai bane kuma gida ya kawoshi (wato
makabarta).Nan take Dan achaba ya ce to su shiga ya ba shi kudinsa. Haka kuwa aka yi, suna shiga abokin namu ya je kan wani kabari yace, Danlami bani
naira tamanin (#80) na ba wa wannan Dan achaban kudinsa, ai kafin ya gama rufe baki
kawai sai suka ga wani hannu ya bullo da naira dari (#100) yace, Karbi wannan ka ba shi, ya ba mu chanji, ni ma ragowar kudina ke nan.
Ai da Saurayin nan da Dan achaba sai kowa ya cika rigarsa da iska yayi takansa. Ashe wani
Mahaukaci ne yazo ya kwanta a ciki, banza ta kori wofi ke nan.
A ganinku, tsakanin saurayin da Dan achaba wa zai fi wani gudu?

Ku turo amsoshi zuwa ga: tsuntsumediaservices@yahoo.co.uk



                       Barawon Takobi

Daga  Bashiru Saleh

Wani barawo ne ya shiga wani gida sata.Dayake dare ne yana cikin lalube sai yaji ya tabo wani sharbeben takobi a rataye.Da har zai dauka sai canja shawara yace ba sai na gama sace kayan gida sannan sai in zo in dauke wannan takobin,don daga ji zayyi tsada sosai.
Bayan ya gama sace kaya ne sai ya dawo domin daukar wannan takobi,ga mamakin sa da ya shafo wajen sai yaji ba takobin sai dai gidan takobin.

Mai ya kamata barawon yayi ?

Ku turo amsoshi zuwa ga: tsuntsumediaservices@yahoo.co.uk






No comments:

Post a Comment